Yadda sojojin Najeriya suka dirar wa sansanin Bello Turji a jihar Sokoto

Spread the love

Rahotanni da ke fitowa daga yankin Sabon Birni na jihar Sakoto na cewa dakarun sojin na can suna fafatawa gaba da gaba da tungar gawurtaccen ɗanfashin daji Bello.

Bayanai sun nuna cewa sojojin sun shiga dajin ne tare da haɗin gwiwar mayaƙan sa-kai da kuma dakarun tsaron da gwamnatin jihar ta Sokoto ta horar.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa jami’an tsaron sun yi wa ‘yan bindigar ƙofar rago a wasu wurare na yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mazauna garin Mera da ke jihar Kebbi suka ce dakarun sojin ƙasar sun fatattaki ‘yan ƙungiyar Lakurawa da suka ɓulla a yankin a baya-bayan nan.

A ranar Larabar da ta gabata ma sai da babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribado, ya sha alwashin cewa dakarun ƙasar za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin fatattakar duka ‘yanbindigar da suka addabi ƙasar.

‘Yau kwana huɗu sojoji na rarakar dabar Turji’

Bayanai na cewa a baya-bayan nan Bello Turji ya yi ƙaura daga wasu yankunan jihar Zamfara, inda ya koma tsakanin ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni na jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun ce dakarun na Najeriya sun kwashe tsawon kwana huɗu suna luguden wuta kan dabar ta Bello Turji.

Wani mutumin yankin da BBC ta zanta da shi ya shaida cewa sun kwashe tsawon kwanakin suna jin ƙarar harbe-harbe a yankunan.

”Ƙarar bindiga tamkar muna Gaza, kullun tun ƙarfe taran dare za ka ji ƙarar bindigogi na tashi, wata bindigar idan an harba yadda ka sa ɗakunanmu za su tashi”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa yankunan da sojoji n suka fi mayar da hankali a luguden wutar sun haɗa da dazukan ƙauyukan Tara da Gatawa da Kurawa da Fadamar Sabon Birnin.

Mutumin – wanda a lokacin zantawarsa da BBC ake iya jin ƙarar harbe-harben bindiga – ya ce sojojin sun far wa dabar Turjin ne bayan da suka samu bayan cewa ya koma yankin Isa da Sabon Birni.

Ya ƙara da cewa bisa bayanan da mazauna garin ke samu, shi ne dakarun na Najeriya na cin nasara a wannna gumurzu.

Kodayake ya ce ba zai iya bayar da cikakken bayanin hasarar rayuka ba, amma ya ce bayanan da suke samu suna daɗaɗa musu rai.

Bello Turji na ɗaya daga cikin gawurtattun ‘yanbindiga da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo, sakamakon yadda ya addabi mutanen wasu sassan arewacin Najeriya.

Turji ya yi ƙaurin suna a yankin arewa maso yammacin ƙasar, musamman jihohin Zamfara da Sokoto, inda yake kai hare-hare kan ƙauyuka da matafiya tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

A wasu lokutan kuma yakan aza wa garuruwa harajin miliyoyn kuɗi, idan suna son tsira daga farmakin yaransa.

Ko a watan Satumban da ya gabata ma sai da ya aza wa mazauna garin Moriki na yankin Shinkafi diyyar naira miliyan 50 na dabbobinsa da wani kwamandan rundunar sojin Najeriya da aka aika garinsu ya kashe a yayin faɗa da ‘yan bindigar, ko da yake daga baya jama’ar sun roki Turjin ya sassauta masu zuwa Naira miliyan 30.

Lamarin da ya sa mutanen yankunan da yake yawan kai wa hare-hare suka ƙaurace wa garuruwansu tare da komawa zaman gudun hijira a wasu yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *