Daga Ibrahim Hamisu
Kamfanin shirya Finafinai na M. Soja Concept NIG. LTD ya na cigaba da daukar sabon Fim din comedy mai dogon zango mai suna JIKOKIN MAI GARI.
Fim din wanda yanzu yanzu haka ake daukarsa a guraren Daban-daban a jihar Kano, ana sa ran fitowarsa nan ba da dadewa ba.
- Kano: Matashin Da Ake Zargi Da Kunna Wa Mutane Wuta Ya Amsa Laifuka 3 A Gaban Kotun Musulinci
- Ƙasashen Afirka biyar masu ƙarfin tattalin arziƙi da al’ummarsu ke wahala
Mujahid M. Soja wanda shi ne Daraktan fim din kuma shi ne ya kirkiro labarin, ya bayyana cewa an gina labarin ne don nishdartarwa da fadakarwa iri iri,
“Jikokin Mai Gari fim ne da aka gina shi akan wasu yara biyu da suka kasance jikoki ga mai àgarin garin, inda suka addabi kowa a garin, ta yadda har ƙona garin Fulani suka yi kuma fitinar ta su ta samo asali ne saboda wani buri da suke so su cimma, kuma duka suna yi ne saboda Mai Gari ya gaji da su ya kore su,”… Inji Mujahid M. Soja
Kamilu Ibrahim DanHausa shi ne Furodusa na fim din ya bayyana cewa an yi kokarin wajen sanya Jarumai da za su ja hankali tun daga kan yara da matasa da kuma Tsofaffi da za su ja hankalin yan kallo,
DanHausa ya ƙara da cewa “Fim ne da zai fadakar ya nishadantar da al’umma domin an yi shiri na musamman”.
Fim din da ake daukar sa a ARTV da garin Langel, fitattun jarumai da dama sun taka rawa a ciki kamar A’isha Najamu, Sulaiman Bosho da Billisu Be Safana da Adam M. Adam da Samira Sani da sauran Jarumai maza da mata.