Yadda Waƙar Rarara Ta Ɗaga Darajar Fatima Mai Zogale

Spread the love

Fatima Mai Zogale, wata mata ce da kimanin wata ɗaya da ya gabata, babu wanda ya san ta sai dai na kusa da ita ko masu zuwa sayen zogale a inda take a karkashin wata mace a Abuja.

Amma cikin mako biyu zuwa uku, Allah Ya ɗaga likafarta, inda ko google ka shiga da zarar ka sa Fatima, zai ƙarasa maka da Mai Zogale.

Sannan kafofin sadarwa na zamani duk sun cika da batunta.

Fitattun marubuta da farfesoshi sun yi rubutu tare da yin sharhi a kanta da kuma wakar da aka yi mata.

Yadda lamarin ya samo asali

A ranar Larabar makon jiya ne fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya fitar da wata waka mai suna Fatima Mai Zogale.

Ya fitar da wakar ce a daidai lokacin da ake tsaka da tattauna zargin da Adam A. Zango ya yi a kansa cewa, sun raka shi wurare ya karɓi manyan kudade, amma ya sam musu ’yan kaɗan.

Na kusa da shi sun fara mayar da martani, inda su ma na kusa da Zango suka mayar da martani, sai ya fitar da wakar wadda ta dauke hankalin mutane.

Kafin wakar ta Fatima Mai Zogale, ya yi wakar Maryama kimanin mako takwas da suka gabata.

Kafin wannan, ya yi wakar A’isha, wadda aka sa a fim ɗin ‘A cikin biyu’ na A’ishatu Humaira, inda aka yi tunanin saboda ita A’isha Humaira ya yi wakar.

Yadda ya yi wakokin guda uku a jere, wadanda dukkansu na nanaye ya sa wasu suke mamakin yadda ya fara shiga bangaren, wanda ba a san shi a ciki ba.

Shi dai Rarara ya fi fice a ɓangaren waƙoƙin siyasa ne, wanda hakan ya sa wasu suke masa shaguben cewa wakar ta fara kare masa ne shi ya sa ya fara komawa nanaye.

Wakar A’isha ta dauki hankali, inda aka fara zargin soyayyar da ke tsakaninsa A’ishatu Humaira ce ta fito fili.

Daukakar Fatima Mai Zogale

Ko da ya fitar da wakar, babu wanda ya san wace ce Fatima Mai Zogale, inda da farko aka fara tattauna yanayin tsarin wakar da baitocinta.

Wasu sun bayyana cewa, bangaren wakar nanaye ba na Rarara ba ne, domin a cewarsu ya yi amfani da wasu kalamai da babu su a kokarinsa na fitar da kafiya.

Daga cikin wadanda suka dan kushe wakar, akwai dan jarida kuma fitaccen mai rubutu a kafafen sadarwa, Yakubu Musa da matashin dan jarida Aliyu Dahiru Aliyu.

Hakan ya sa Farfesa Ibrahim Malumfashi ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Zuwa ga Aliyu

Dahiru Aliyu da kuma Yakubu Musa dangane da waƙar Fatima Mai Zogale ta Rarara.

“Zan so ku sake sauraren waƙar Dauda Kahutu Rarara ta Fatima Mai Zogale da kyau, ni dai abin da kuka ji kuka rubuta, ƙila ba shi ne ni na ji ba, ba kuma wai don ina son kare Rarara ba, sai dai don a yi wa adabin adalci! Mu tattauna in kuna da lokaci!”

A ƙarƙashin wannan rubutu an samu martani 141, wanda ya kara jawo hankalin mutane game da wakar.

Ana cikin haka ne sai Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Watsa Labarai bangaren jarida, Malam Abdul’aziz Abdul’aziz ya rubuta a shafinsa cewa, “Uwar ɗakin Mai Zogale ta sallami Fatima a dalilin waƙar.”

Wannan rubutun na Abdul’aziz ya samu martani 1,100, sannan an yada shi sau 247.

Wannan ne ya tayar da kura a kafofin sadarwa, inda aka fara neman wace ce Fatima Mai Zogalen nan.

Ana cikin haka ne uwar ɗakin Fatima ta fito ta bayyana cewa, ta sallami ’yar aikinta, tana mai cewa Fatimar ce da kanta ta ce za ta yi aure, don haka za ta daina aiki.

Uwar dakin mai suna A’isha ta bayyana a cikin wani bidiyo cewa, suna zaune lafiya kalau, sai Fatima ta ce za ta daina aiki domin za ta je ta yi aure.

Wannan ya sa aka fara ƙaryata wadanda suka yada cewa an kori Fatima daga aiki.

Sai dai ana cikin haka ne kuma sai Fatima ta saki wani bidiyo, inda a ciki ta bayyana cewa lallai sallamarta A’isha ta yi saboda wakar ta Rarara.

A cikin bidiyon ta ce, “Na ji tsohuwar uwar ɗakina tana cewa ba kora ta ta yi ba, cewa na mata ƙarya. Wannan shi ne karo na biyu muna samun matsala da ita.

“A lokacin azumi, wani mutum ya ba ni kyautar atamfa guda biyu, sai ta ce dole sai na ba ta ɗaya, ni kuma na ƙi, saboda mutumin ya ce in bai wa mahaifiyata ɗaya.

“A wannan lokacin ta sallame ni daga aiki saboda atamfar.

“Bayan azumi ta sake dawo da ni. Bayan mako biyu da dawowata ce mawaƙi Rarara ya zo sayen zogale.

“Sai na ce masa na dade ina ƙaunar wakokinsa, ya sayi zogale ya tafi. Bayan kwana biyu kawai sai na ji wakar Fatima Mai Zogale.

“Ni ba ni da babbar waya, wani ne ya kawo min wakar. Sai kuma aka zo aka dauke ni hoto ina zuba zogale.

“Nan ne kuma A’isha ta ce ta ji wata wakar Fatima Mai Zogale, ni ce aka yi wa wakar?

“Na ce kada ta damu ai nasararmu ce duka saboda an tallata mana zogalenmu.

“Sai ta ce me ya sa zan bari a yi min waka ba tare da izininta ba? Ta yi fushi sosai.

“Washegari ta kira ni, ta ce ta sallame ni daga aiki. Cikin kuka na ba ta hakuri, amma ta ki,” in ji ta.

Ana cikin haka fitaccen marubuci, Malam Ibrahim Sheme ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, Rarara zai taimaka wa Fatima Mai Zogale, sannan shi ma zai ba ta gudunmawa.

Sannan a ranar Litinin da ta gabata, an ga Fatima Mai Zogale a wani taron da aka ce Dauda Kahutu Rarara ya shirya wa masoyansa, inda ta je a matsayin babbar baƙuwa.

A taron, Zogale aka riƙa ci, sannan ana ta rera wakar Fatima Mai Zogale.

Da yake tattaunawa da ’yan jarida bayan taron, Rarara ya bayyana cewa, wasu manyan mutane irin su Minista T. Gwarzo da sauransu duk za su taimaka mata.

Ya ce, bai san cewa wajen zogalen ba nata ba ne, amma yanzu za su taimaka mata su buɗe nata a Kaduna da Kano da Abuja.

Labarin Fatima wadda ’yar asalin garin Akilibu ne da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja a Jihar Kaduna, ya zama labarin a dare datya Allah kan yi Bature, inda ta samu ɗaukaka a sanadiyar waka.

Tuni ta bude shafin Instagaram, inda a ranar Talata da Aminiya ta leƙa, tana da mabiya 2,514, tana bin mutum ɗaya, sannan ta wallafa abubuwa uku kacal.

AMINIYA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *