Yadda ’Yan Wasan Super Eagles Suka Kunyata ’Yan Nijeriya

Spread the love

Ayarin ’yan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, Super Eagles sun kunyata ’yan Nijeriya a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya, inda ’yan wasan Jamhuriyyar Benin suka doke su da ci 2-1 a wasan da suka buga a Abidjan a ranar Litinin ta makon jiya.

Kungiyar Super Eagles ce ta fara cin kwallo a minti na 27 da fara wasan ta hannun Raphael Onyedika.

To sai dai minti 10 kacal ’yan wasan Benin suka farke ta hannun Jodel Dossou, sannan Steve Mounie ya kara ta biyu ana daf da zuwa hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Benin, wadda ita ce ta 97 a teburin FIFA, ta koma ta daya a Rukuni na Uku da maki bakwai, sai Lesotho ta 149 a teburin FIFA ke biye da ita da maki biyar, yayin da Rwanda ta 131 a teburin FIFA ta zama ta uku da maki hudu.

Afirka ta Kudu wadda ita ce kasa ta 59 wajen iya taka leda a duniya, ita ce ta hudu da maki hudu.

Sai babbar yaya Nijeriya wadda ita ce kasa ta 30 a teburin FIFA ta zama ta biyar da maki uku yayin da Zimbabwe wadda ita ce kasa ta 122 a teburin FIFA take karshe a rukunin da maki biyu.

Nijeriya ta dai ta sha kunya ne a hannun tsohon kocinta Mista Gernot Rohr, wanda ya fara aiki da ita a Agustan 2016.

Rohr ya fara wasa da kafar dama a wannan gasa da cin wasan farko inda ya doke Tanzaniya a Uyo.

Ya fara rashin nasara ranar 10 ga watan Yuni a hannun Afirka ta Kudu da cin 2-0.

Ranar 7 ga watan Oktoban 2017, shi ne na farko daga Afirka da ya samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya a Rasha a shekarar 2018 lokacin yana kocin Nijeriya.

Haka kuma Rohr ya ja ragamar Super Eagles zuwa mataki na uku a gasar cin Kofin Afirka a shekarar 2019, kafin a kore shi a ranar 12 ga watan Disamban 2021.

An kuma sallame shi ne duk da ya kai Nijeriya gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2021 da karawar cike gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *