“Babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah da kuma duk waɗanda suka taya mu addu’a,” wannan ne abin da Aisha Kabir, wadda aka fi sani da Chefsafmar, ta faɗa wa BBC Hausa bayan yaranta da aka sace sun samu ‘yanci.
A daren Talatar makon jiya ne masu garkuwa da mutane suka faɗa gidan su Aisha Kabir, inda suka yi awon gaba da ƴaƴanta huɗu – uku mata, da namiji ɗaya wanda bai ƙarasa shekara biyu ba.
Da take tabbatar da sako yaran, Aisha, ta ce: “Na ji farin ciki sosai. Alhamdulillah, Allah ya warware ƙullin da ke cikin zuciyata, domin da suka tafi wani abu na ji ya tokare min zuciya, amma ina ganinsu sai na ji kamar an cire min abin.”
Labarin sace yaran na cikin a ayyukan ‘yanbindiga na baya-bayan nan da suka ɗaga hankalin mazauna arewacin Najeriya, musamman bayan da aka fara batun cewa masu garkuwan sun nemi a ba su kuɗin fansa naira miliyan 300 ko kuma su illata yaran.
Mahaifiyar yaran ta faɗa wa BBC cewa suna cikin ƙoshin lafiya, sai dai “sun sha cizon sauro, sannan ƙafafunsu duk sun kumbura”.
“Amma da ɗan ƙaramin wato Hamad ya gan ni, sai ya fara cewa ‘mama, baba’ amma kuma yana ɗan yin baya-baya kamar a tsorace yake. Amma dai Alhamdulillahi,” a cewarta.
A game yadda suka samu labarin kuɓutar yaran, ta ce a bakin mutane suka fara ji.
“Ba mu san abin da ke faruwa ba saboda kafin mu tafi mutane suna ta kira na suna cewa an ce an karɓo yaranmu. Bayan kusan awa ɗaya ko biyu ana kiranmu a waya, sai aka zo aka saka mu a mota, shi ma ba a faɗi inda za mu je ba. Aka kai mu inda aka ajiye su.”
Sai dai ta ce sun biya wani abu a matsayin kuɗin fansa.
- Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a da majalisa su yi gyara a dokar haraji
- An shiga ruɗanin siyasa a Koriya ta Kudu bayan shugaban ƙasa ya ayyana dokar soji
“A kwana na shida, da ma suna ta kiranmu a waya suna neman a ba su kuɗi. To ba mu da kuɗin da suke nema. Sai suka ce mu kawo naira miliyan 25, kuma ba mu da su. Daga baya suka tambaya nawa ne a ƙasa, aka ce musu akwai naira miliyan takwas, suka ce a kawo a daren ranar ta shida.
“Da aka kai kuɗin sai suka faɗa wa waɗanda suka kai cewa ba za su bayar da yaran ba, sai an ciko kuɗi naira miliyan 17.”
Ta ƙara da cewa da aka faɗa mata wannan maganar “sai na ji tamkar a ranar aka sace yaran saboda komai ya dawo min sabo”.
A gefe guda kuma, Aisha ta ce gwamnatin jihar ba ta biya kuɗin fansa ba kafin karɓo yaran.
‘Tafiya kamar nisan Kaduna zuwa Zariya’
Kasancewar iyayen ba su gida lokacin da maharan suka ɗauki yaran, sai a yanzu ne aka samu labarin takamaimai yadda aka sace su.
Mahaifiyar tasu ta ce yaran sun faɗa musu cewa bayan sun gama addu’o’i sun kwanta, kawai sai suka ga ƴanbindiga a kansu, kuma suka tafi da su.
“Babbar ta ce mana sun yi tafiya mai nisan da za ta kai daga nan [Kaduna] zuwa Zariya a ƙafa. Safa da Amina, su ne manya, su suka riƙa goya Hamad. Idan wannan ya gaji, sai ya ba wannan. Idan sun ce wa mutanen su ɗan taimaka musu su ɗauke shi, sai su ƙi.
“Da muka tambaye su, sun ce ana ba su abincin safe da rana da dare amma taliya ce da manja. Shi kuma ƙaramin da yake yana son shayi, idan ya ce a ba shi shayi, sai su dake shi.”
A ƙarshe ta yi godiya ga mutane, tana mai cewa: “Babu abin da zan ce wa mutane sai dai godiya. Allah ya saka wa kowa da alheri, ya biya wa kowa buƙatunsa na alheri.”
BBCHAUSA