Yahaya Bello ya nemi a mayar da shari’ar da ake yi masa zuwa Kogi

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya buƙaci alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya mayar da shari’ar da ake yi masa kan zargin badaƙalar kuɗi zuwa jihar Kogi.

Yayaha Bello ya ce zai fi son agurfanar da shi a Lokoja – wurin da ake zargin ya aikata laifin – saɓanin Abuja da ake yi masa a yanzu.

Tsohon gwamnan ya bayyana buƙatar tasa ne a ranar Alhamis ta bakin lauyansa a lokacin zaman kotun na ranar Alhamis.

Lauyan mai suna Adeola Adedipe (SAN) ya ce sun nemi buƙatar ne saboda babbar kotun tarayya da ke Lokoja na da damar sauraron shai’ar da ake yi wa tsohon gwamnan.

Adedipe ya ce tawagar lauyoyin tsohon gwamnan na jiran amsa daga babban alƙalin kan buƙatar tasu.

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban shari’a bisa tuhume-tuhume 19 da suka jiɓanci ɓarnatar da dukiya.

EFCC na tuhuar gwamnan da badaƙalar kuɗi da suka kai naira biliyan 80.2.

Yahaya Bello ya mulki jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, tsawon wa’adi biyu daga shekarar 2016 zuwa 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *