Yan bindiga sun kai hare-hare tare da sace fiye da 30 a Kaduna

Spread the love

Rahotonni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun auka wa garuruwan Gwada da Kwassam a ƙananan hukumomin Igabi da Kauru da ke jihar Kaduna, inda suka kashe mutum tara da raunata a ƙalla bakwai, tare kuma da yi garkuwa da fiye da mutum 30, ciki har da tsohon daraktan babban bankin ƙasar CBN.

Cikin wata sanarwa da kakakin Ƙungiyar Al’ummomin Yankin Kudancin Kaduna, (SOKAPU), Josiah Abraks, ya fitar ya tabbatar da harin ‘yan bindigar a garin Kwassam .

Ya ce maharan sun yi garkuwa da kimanin mutum 50 a wani hari da suka kai ƙauyen Sabon Layi.

Abraks ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro da su ɗauki mataki kan maharan da ke yawan kai wa yankunan kudancin Kaduna hare-hare.

Hukumar NAFDAC ta jagoranci garkame shagunan yan Magani 700 a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

To sai dai cikin wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta fitar ta hannun kwamishin lura da harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, gwamnatin ta tabbatar da hare-haren sai da ba ta yi ƙarin haske kan waɗanda suka mutu ko aka sace ba.

Sanarwar ta ambato gwamnan jihar, Uba Sani na Allah wadai da hare-haren tare da jajanta wa mutanen da lamarin ya shafa, yana mai kira ga sojoji da su tsananta hare-hare kan ‘yanbindigar da ke addaban yankin.

Gwamnan ya kuma aike da tawagar wakilan gwamnati ƙarƙashin jagorancin kwamishin lura da al’amuran tsaron cikin gida, garin da lamarin ya faru, inda suka gana da sarakunan gargajiyar yankin da jagororin addini na yankin.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke sace mutane domin neman kuɗin fansa.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *