‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu tare iyalansu a Kaduna

Spread the love

Masu garkuwa da mutane sun sace ‘yan jarida biyu tare da matansa da ‘ya’yansu a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, NUJ reshen jihar ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare a gidajensu a unguwar Danhono da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare lokacin da ‘yan bindigar suka shiga unguwar riƙe da makamai suna harbin kan mai tsautsayi.

Ƙungiyar NUJ ta kaɗu da labarin garkuwa da ‘yan jaridun biyu da ta ce suna aiki ne da jaridun ‘The Nation’ da kuma ‘The Blue Print’ da kuma iyalan nasu.

Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare da yin kira ga jami’an tsaro a jihar su jajirce wajen kuɓutar da su.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda a wasu lokuta ‘yan bindiga ke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Ko a watan Maris na wannan shekarar ma wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar Kuriga da ke jihar, tare da sace ɗalibai fiye da 100, kodayake daga baya ukumomi sun kuɓutar da su bayan shafe wasu kwanaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *