Kungiyar ‘yan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
Darajar takardar kudin Najeriya – Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin kasar.
A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.
Ba mu amince da wasu mombobin kwamitin albashi ba – Shugaban NLC
Yan bindiga sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan gida daya a Abuja
Kungiyar ‘yan canji ta alakanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kudade ta Intanet irin na Crypto da ake kira Binance
Hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta hana ‘yan Najeriya hulda da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.