Wasu ’yan daba sun ƙone Ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Akwa Ibom (AKISIEC), da ke karamar hukumar Ibiono Ibom.
Rundunar ’yan sanda jihar, ta tabbatar da kai harin, wanda ta ce an yi hakan ne domin hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Da ta ke zantawa da manema labarai a Uyo a ranar Asabar, kakakin rundunar, ASP Timfon John, ta ce, “Wasu ’yan daba sun ƙone wani ɓangare na ofishin AKISIEC a Ibiono Ibom.