Wasu mutane biyu da ke zargi da laifin fashi da makami a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar duro wa daga wani ginin bene mai hawa biyu a kotun da ke sauraron tuhumar da ake yi masu.
Mai gabatar da ƙara a Kotun Majastare ta Iyaganku da ke Ibadan, Sufeton dan sanda Femi Omilana ya ce, tun cikin shekarar 2023 kotu ta bayar da umarnin tsare waɗanda ake zargin.
- Sojojin Nijar sun kama Ɓaleri, ɗan bindigar da Najeriya ke nema
- Sojojin Nijar sun kama Ɓaleri, ɗan bindigar da Najeriya ke nema
Wadanda ake zargin sun hada da, Damilare Adeniran da abokinsa Victor, tare da wasu Mutane uku da Suka yi amfani da bindigu da wasu makamai wajen yi wa jama’a fashi.
Ya ce, waɗannan yan fashi sun kuɓuce daga hannun jami’an tsaro a cikin Kotun ne suka yi kasadar tsallaka tagar Kotun da suka duro ƙasa inda suka samu munanan raunuka a sassan jikinsu.
Sufeto Omilana ya ce yan fashin sun duro ƙasa ne a daidai lokacin da Alkali G.
Oladele na Kotun Majastare yake sauraron
ƙarar da ake tuhumarsu a ranar Laraba.
Ya ce an garzaya da su zuwa Asibitin don kula da lafiyarsu inda za a ci gaba da tsare su a gidajen yari.
Alƙalin Kotun ya ɗage ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi musu zuwa ranar 8 ga watan Yuli mai zuwa.