Yan Jaridar Portugal Sun Fara Yajin Aiki Karon Farko Cikin Shekaru 42.

Spread the love

Wata kungiyar kwadago a kasar Portugal, ta bukaci dukkanin yan jaridar kasar, da su shiga yajin aikin kwana daya, bisa karancin albashin da ake biyan ma’aikata da kuma rashin aikin yi da ake fama da shi a kasar.

Wannan yajin aikin shi ne na farko a Portugal cikin shekaru 42.

Tun a shekarar 1982 aka yi yajin aikin gama gari na yan jaridu a kasar.

Wannan dai na zuwa bayan kafar yada labarai ta Portugal, Global Media, ta bada sanarwar tabarbarewar tattalin arziki, wanda ka iya shafar ma’aikatan ta 20 ciki harda yan jarida 10.

Yar’Adua ya zama sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya

Majalisa ta yi karatu na biyu ga kudirin bai wa daliban Najeriya bashin karatu
Ma su yajin aikin sun yi kira da aka mu su albashi don samun saukin hauhawar farashin kayayyaki bisa bin ka’idoji na karin albashin.

Kungiyar yan jaridun da ta yi kiran yajin aikin, ta bayyana cewa rashin aikin yi da kin kara mu su albashi zai kawo koma baya ga yan kasar wajen samun labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *