Kungiyar masu fiton kayayyaki ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bude tashar kan iyaka ta Lolo da ke tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.
Kungiyar ta yi barazanar rufe dukannin kasuwanni a yankin arewacin Najeriya muddin ba a dauki matakin bude bodar ba.
Ta ce matakin gwamnatin Najeriya na rufe tashar na barazanar durkusar da miliyoyin ‘yan kasuwa da ke yankin arewacin Najeriya.
A wani taron da manema labarai, a Kano shugaban kungiyar Alhaji Muftahu Ya’u ya ce tashar kan Iyaka ta Lolo ba ta cikin jerin tashoshin fiton kayayyaki na kan tudu da gwamnatin Najeriya ta rufe, la’akari da cewa, wannan tasha bata hada kan iya da Jamhuriyar Nijar ba, don haka bai kamata matakin kungiyar ECOWAS ya shafe ta ba.
Ya ce yanzu haka akwai kwantenoni fiye da 700 jibge a tashar ta Lolo makare da kayayyakin ‘yan kasuwa kuma wasu daga cikinsu na dauke ne da kayayyakin da ka iya lalacewa ko lokacin amfanin su ya wuce.
Ya ce ita kanta gwamnatin tarayyar na asarar naira biliyan 13 kudin haraji a kowane wata sakamakon rufe boda ta Lolo.
A cewar, shugaban kungiyar lokaci ya yi da shugabannin arewa , musamman masu rike da madafun iko, gwamnoni yan majalisar dokoki su fito su yi magana a bude bodar ta Lolo.