Hadaddiyar kungiyar Yan kasuwar magani ta kasa reshen jahar Kano, ta koka da girman asarar da suka tabka cikin watanni biyu kachal , sakamakon rufe mu su shagunan kasuwancin su da hukumomi suka yi.
Yan kasuwar sun gudanar da wani tattakai zuwa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar litinin, domin shaida mata girman asarar da suka yi , da kuma rashin sanin makomar matasan, dake zaune babu sana’ar yi, Wanda hakan ke Kara yi wa matasan barazanar fadawa aiyuka marasa kyau.
- Ma’aikacin Binance ya tsere daga Najeriya – Rahotanni
- Kotu Ta Haramta Wa Murja Kunya Amfani Da Shafukan Sada Zumunta
Shugaban kungiyar Alhaji Musbahu Yahya Khalid, ya shaida wa jaridar www.idongari.ng, cewar yanzu wasu daga cikinsu abincin yau da Kullum nema yake ya gagare su.
Musbahu Khalid ya ce hatta baturan Sola dake cikin shagunan Yan kasuwar kamawa suke yi da wuta, kuma kayansu na watan Fabarairu zuwa Maris 2024 , wa’adin amfani dasu ya kare kuma babu Wanda zai biya su.
” Ahalin da ake ciki na tsananin rayuwa, tsawon Wata biyu, a rufe wa mutum Shago to me za mu yi , kuma mu bama son tashin hankali” Musbahu Khalid “.
Ya Kara da cewa, bai kamata idan ba a taimaki mai Sana’a ba, to bai kamata a lalata samun sa ba.
” magani ba Tumatur ba ne , da zaka dobe shi ka zuba a kasa , tsawon wadannan lokatun da aka kulle zafi ya yi yawa, Solar da muke sanya wa domin sanyaya dakunan maganin da muke siyarwa yanzu an kasheta” Musbahu Yahya “.
” So ake mu Kama sata a Kama mu, mu abunda muka sani shi ne , Sana’a kuma ita muka rike”.
Ya ce sunje wajen gwamnan jahar Kano Engr. abba Kabir Yusuf, a matsayin sa na shugaban rundunonin tsaro, ya shiga cikin lamarin don a bude mu su shagunan su.
“Mu muka kafa wannan gwamnatin da gumummu, karfe ukun dare Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce mu fito mu tafi INEC kuma muka je aka tabbatar , haka ana shari’a tun daga Kano muke bin shari’ar babu wajen da ba muje munyi sallah ba , don ya samu nasara a kotu, ko shaida ne da aka samu nasarar mun kashe kudi sama da naira miliyan biyar , wajen taron Gwamna Abba Kabir Yusuf, Wanda muke zaton zai yi abubuwa na alkairi sai kuma aka Fara zungure mu”. Musbahu Khalid”.
A cewar Musbahu Khalid, kasuwar Dangora da ake cewa su koma , ba ta gwamnati ba ce , ta wasu mutane ce siraru da suken yin amfani dasu wajen yin kasuwanci, sannan wajen ana siyar da rumfana daya naira miliyan arba’in , akwai kuma mu ta naira miliyan saba’in , inda Masu karamin jari ba za su iya Kama wa ba.
A kwanakin baya ne Wata babbar kotun tarayya a birnin Kano, ta umarce su da su tashi, su koma kasuwar Dangora a yankin karamar hukumar Kumbotso.
Ana zargin Yan maganin da shigo da gurbatattun magani, da miyagun kwayoyi, zargin da suka sha musanta wa.
Ma su sharhi kan al’amuran yau sa Kullum na ganin kokawar Yan maganin kasuwar Dangoro, ba zai haifar da Da mai ido, bisa zargin za a Samu yawaitar siyar da magungunan a unguwanni.