Wata Tawagar masu motar Kurkura sun gudanar da zanga-zanga a bakin ofishin Karota dake Kofar Nassarawa a yau Talata.
Yan ƙurƙurar sun tare hanyar dake zuwa titin Obasanjo karkashin Gadar sama ta kofar Nassarawa inda suke ta neman gwamnati ta kawo musu dauki kan gashin kumar da suka ce hukumar Karota na yi musu.
Nasiru Muhd sakataren kungiyar yan Ƙurƙura ta jihar Kano ya ce sun fito wannan zanga-zanga zangar ne saboda wata sitika da aka kara kakaba musu ba gaira babu dalili.
- Ana takun-saƙa tsakanin manyan sarakunan Yarabawa biyu
- Zaben Cike Gurbi: Cikin Mutane 333 Da Muka Gurfanar Harda Mukarraban Gwamnati- CP Ibrahim Bakori
Ya kara da cewar an yi musu sitika ta kwali wata 8, a baya suna kuma siya! Sai kuma yanzu aka kara kirkiro musu karin wata wai ita GTB! Kuma mu ba ko ina muke zuwa ba aikinmu baya wuce cikin garin Kano, kuma ace sai mun sake siyan wannan” akan dubu 8, bayan wannan.
”Don haka muke kira da Mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf da ya kawo mana ɗauki idan kuma ba so ake mu koma masu zaman banza ba”.