Yan majalisar Amurka sun buƙaci Shugaba Biden ya sa baki a saki shugaban Binance da ke tsare a Najeriya

Spread the love

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka 16 sun rubuta wasiƙar koke zuwa ga shugaban ƙasar, Joe Biden, suna neman a saki shugaban kamfanin hada-hadar kuɗin Kirifto na Binance, Tigran Gambaryan, daga Najeriya don ya koma gida Amurka.

‘Yan majalisar sun yi zargin cewa Mista Gambaryan na cikin mawuyacin hali a inda ake tsare da shi.

Gwamnatin Najeriya ce dai ta kama shugaban kamfanin na Binance, kuma ta tuhume shi tare da kamfanin nasa, game da rashin biyan harajin sayen kayayyaki na VAT da sauran wasu laifuka.

Gwamnatin Najeriyar ta ce ana bin matakan da suka kamata a shari’ar da ake yi masa bisa tsarin dokokin ƙasarta.

‘Yan majalisar dokokin 16 da suka ce suna magana ne da yawun iyalan shugaban kamfanin na Binance, Mista Tigran Gambaryan, da sauran Amurkawan da abin ya dama, sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta mayar da shi Amurka.

Saboda a ganin su ana tsare da shi ne ba bisa ƙa’ida ba, cikin wani mummunan yanayi, da kuma rashin ƙoshin lafiya, abin da suke ganin yana cike da hatsari ga rayuwarsa.

A cikin watan Fabrairun da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta cafke shugaban kamfanin na Binance, tare da shugaban kamfanoin nasa a nahiyar Afirka, Nadeem An-jar-walla, wanda ya tsere a ranar 22 ga watan Maris da ya gabata, daga inda jami’an tsaro ke tsaro da su.

Gwamnatin Najeriyar na tuhumar Mista Gambaryan da kamfaninsa, da zargin kauce wa biyan harajin da akan cire na sayen kayayyaki, da harajin kuɗin shiga na kamfanoni , da kuma taimaka wa abokan hulɗa wajen bijire wa biyan haraji.

‘Yan majalisar dokokin Amurkar sun yi tsokaci cewa, sun gabatar da bukatar tasu ce don a ceci rayuwar Mista Tigran Gambaryan, tun ba a makara ba.

A ɓangaren gwamnatin Najeriya, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya shaida wa manema labarai, cewa ana bin matakan da dokokin ƙasar suka tanada, tare da hujjoji da shaidu a shari’ar da ake yi wa shugaban kamfanin na Binance, game da zargin aikata miyagun laifukan yi wa tattalin arziki zagon ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *