Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta gabatar wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuɗin da suka tara daga albashinsu domin ba da tasu gudummawar wajen rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.
Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ne ya bayyana hakan yayin zaman majalaisar a yau Alhamis, yana mai cewa kuɗin sun kai naira miliyan 704.91.
Ya ce za su yi hakan ne a ranar 31 ga watan Disamban 2024. Tun a watan Yuli ne ‘yanmajalisar suka yi alƙawarin sadaukar da rabin albashinsu domin taimakawa saboda cire tallafin man fetur.
“Ina farin cikin shaida muku cewa zuwa yanzu mun tara naira N704,907,578.82,” in ji Tajudeen.
“A ranar 31 ga watan Disamba, zan jagoranci shugabannin majalisa domin kai wa shugaban ƙasa kuɗin da zimmar yin amfani da su wajen tallafa wa mabuƙata.”
- NAFDAC ta rufe wata kasuwa a Aba bayan gano kayayyakin abinci na jabu na N5bn
- Akpabio ya buƙaci Tinubu ya ja kunnen ministocinsa masu taurin kai