Yan mata sun soki wata tsohuwar doka da wani Lauya ya bankado wadda ta haramta Lefe a Kano

Spread the love

Wasu yan mata a jahar Kano sun koka kan wata tsohuwar doka da ta haramta tsarabe-tsareben aure wato ( Marriage Practices Prohibition Edicts) wadda aka yi tun a mulkin sojoji.

Yan matan sun ajiye, ayar tambayar cewar me yasa ba adaina yin kayan lefen ba tun abaya, sai a wannan lokaci da suke kan ganiyarsu da za su amfana wajen yi mu su aure.

Suma dai wasu iyaye mata sun bayyana cewa suna da yaya mata da maza, amma duk matakin da yafi dace wa aka dauka shi ne daidai.
Idan ba a manta ba idongari.ng, ya ruwaito cewar, wani lauya ne mai suna Abba Hikima Fagge , ya bayyana cewa akwai dokar da ta hana tsarabe-tsaraben aure ciki harda yin kayan Lefe kafin yin aure.

Abba Hikima Fagge ya ce sashi na 315 na kudin tsarin dokokin Nijeriya ya ce, duk da an dawo Jamhuriya ta hudu wato Mulkin Damokuradiya, duk dokar da aka yi a mulkin soja wadda bata saba wa dokar Nijeriya ba, to za a kaddara dokar tananan.

Ya kara da cewa tsohuwar doka ce , tun lokacin mulkin sojoji, wajen shekarar 1980- 1987 wadda aka haramta tsarebe-tsaraben ciki harda lefe da nagani ina so.

Fagge ya ce , duk wanda ya yi lefen tsarabe-tsaraben auren bayan yin waccar dokar , jami’an yan sanda za su iya kama shi sannan su gurfanar da shi a gaban kotu sakamakon saba dokar.

A cewarsa dokar ta tanadi hukuncin dauri na wani lokaci ko cin tarar mutum, ko kuma a hada mutum duka.

Yanzu haka wasu samari a birnin Kano sun bayyana farin cikin su kan wannan batu na tsohuwar doka tun lokacin mulkin sojoji, da lauyan ya bankado, wadanda suke fatan a karkadeta domin lefenne yake hana su yin auren.

Sai dai yan matan sun bayyana rashin jin dadinsu kan wannan lamari, inda suka ce sai dai suma samarin a daina kai musu kayan daki.
Yanzu dai kallo ya koma sama, wajen samari da yan mata kan wannan tsohuwar doka, da ta ke kanshin turare dan goma a wajen samari yan lalle, ko gwamnatin farar hular za ta waiwayi dokar domin yi mata kwaskwarima ko yan mata da samarin a samu mafita daga matsalolin da ake samu na dage-dagen aure sakamakon rashin kayan daki ko kuma lefe.

WWW.IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *