Yan matan Najeriya da aka yi safararsu zuwa Ghana sun koma ƙasar

Spread the love

Hukumar Kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙetare NIDCOM, ta ce an mayar da ‘yan matan ƙasar kimanin 10 da aka yi safararsu zuwa Ghna.

Cikin wata sanarwa da shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafinta na X, ta ce a ranar Juma’a ne ‘yan matan waɗanda aka kuɓutar daga Ghana suka koma ƙasar.

Ta ce ‘yan matan – waɗanda mafi yawansu ‘yan jihar Imo ne – na tare da wakilan gwamnatin jihar.

Ms Dabiri ta ce hukumarta ta samu bayanan ‘yan matan ne daga hukumar yaƙi da safarar bil-adama ta ƙasar (NAPTIP).

‘Yan matan – waɗanda dukansu ‘yan ƙasa da shekara 18 ne – wani mutum ne da ba a ambaci sunansa ba ya yi safararsu zuwa Ghana.

Tuni dai ‘yan sanda Ghana suka cafke mutumin, inda suke ci gaba da gudanar da bincik.

Ms Dabiri kungiyar ‘yan Najeriya mazauna ƙetare reshen ƙasar Ghana ne suka taimaka wajen kuɓutar da yaran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *