Yan Najeriya na da yancin ɗaukar bidiyon ‘yan sanda a bakin aiki: Adejobi

Spread the love

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce yan ƙasar na da damar ɗauar bidiyo da hotunan ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.

Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin sada zumunta ya wallafa, da ya ce ‘yan sanda sun karbi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su, a lokaci da suke binciken ababen hawa.

Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan ‘yan sandan da ke bakin aikin.

Mista Adejobi ya ce duk wanda ‘yan sanda suka ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar ‘yan sanda.

Cikin sakonsa na X da ya wallafa, mista Adejobi ya ce ” ya kama kowanne ɗan sanda ya sani cewa ba laifi ba ne ɗaukar bidiyo ko hotunansu a lokacin da suke bakin aiki”.

Sannan waɗanda suke cin zarafin masu ɗaukarsu hoto ko bidiyo saboda wannan, su daina domin ba laifi ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *