Yan Najeriya na tara kuɗi don ceto yaran da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Yan Najeriya na tara kuɗi don ceto yaran da aka yi garkuwa da su a Abuja Masu amfani da shafukan sada zumunta na ci gaba da neman taimako domin tara kuɗin da za a karɓo wasu iyalai da aka yi garkuwa da su.

A ƙarshen mako ne labarin – garkuwa da wani mutum tare da iyalansa da suka haɗa da yara shida – ya ɓulla.

Lamarin ya kara kamari bayan da masu garkuwar suka kashe daya ɗaga cikin yaran, sabada gaza tara makudan kudaden da masu garkuwar suka buƙata.

Tun da farko ‘yan bindigar sun je gidan mutumin ne a unguwar Bwari da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar 2 ga watan Janairu, inda suka yi garkuwa da mutumin tare da ‘ya’yansa shida, inda suka buƙaci a biya wasu miliyoyin kudi kafin a sake su.

TALLA

Abin da ya sa ‘yan bindigar suka saki mahaifin yaran da nufin ya je nemo kudin fansar ‘ya’yan nasa.

Kasancewar ba shi da dalilin kudin ne ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta suka riƙa wallafa labarin tare da neman taimako a shafukansu da nufin taimaka wa iyalan.

Sakamakon jinkirin da aka samu wajen tara kuɗin ne ma ya sa masu garkuwa suka kashe ɗaya daga cikin ‘ya’yan.

Wannan labari ya ja hankalin mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta, inda aka riƙa bayar da taimako da nufin tara kudin fansar sauran yaran da ke hannun masu garkuwar.

Cikin wadanda suka sa baki a lamarin har da tsohon ministan sadarwar ƙasar Dakta Ali Pantami, wanda ya ce wani aboki kuma ɗan uwansa ya bayar da naira miliyan 50 da nufin ceto yaran.

A sakon da ya wallafa, Pantami ya ce: ”Ni a kan kaina bana goyon bayan biyan kudin fansa ga ɓata-gari, to amma ya bayyana a gare mu sun kashe ‘yarmu Nabeeha jiya, kuma suna yi wa sauran ‘yan uwanta biyar barazana da kisa, kamar yadda mahaifinsu ya shaida min jiya a lokacin da na yi magana da shi”

Satar mutane domin neman kudin fansa dai ba sabon abu ba ne a Najeriya musamman a yankunan arewa maso yammacin kasar da wasu yankunan kudancin ƙasar.

To sai dai ba a cika samun irin hakan a babban birnin tarayyar ƙasar Abuja ba, to amma a baya-bayan nan birnin ya fara fuskantar matsalar, wani abu da masana tsaro ke gani a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *