Yan Najeriya su guji murnar wuce iyaka idan Eagles suka doke Bafana Bafana’

Spread the love

Ofishin jakadancin Najeriya ya shawarci yan kasar da ke zaune a Afirka ta Kudu gabanin wasan da kasashen biyu za su fafata a gasar kwallon Afirka a Ivory Coast.

Sanarwar da ofishin ya fitar ranar Talata ta gargadi yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudun su guji tsokanar takwarorinsu idan Super Eagles ta yi nasara a wasan.

Sanarwar ta nemi “yan Najeriya su kula da kalamansu, su kuma yi taka tsan-tsan game da inda za su kalli wasan musamman a wuraren taron jama’a”.

Ta kara da kira ga yan Najeriyar su guji yin murnar wuce gona da iri da ka iya jawo tashin hankali idan har Najeriya ta doke Afirka ta Kudu.

Shugaban karamar hukumar Nasarawa ya koma NNPP Kwankwasiyya a Kano

Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargadi kungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Ofishin jakadancin ya yi gargadi kan mayar da martani ko ta wace fuska a maimakon haka, ofishin ya bukaci mutanen da abin ya shafa su kai korafi kan duk wani yanayi na tashin hankali ga hukumomin da suka dace.

A ranar Juma’ar da ta wuce, kwallon da Ademola Lookman ya zura a ragar Angola ce ta bai wa Super Eagles shiga zagayen kusa da na karshe a gasar ta Afcon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *