Wani rahoton bincike da hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun bai wa jami’an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 (dala biliyan 1.26) a matsayin cin-hanci a 2023.
Rahoton ya ce ‘yan Najeriyar sun ba da cin-hancin ko kuma rashawa sau miliyan 87, amma adadin ragi ne idan aka kwatanta da miliyan 117 da suka bayar a 2019.
Cikin duka ‘yan Najeriyan da suka ga aƙalla wani jami’in gwamnati ɗaya cikin wata 12 kafin gudanar da binciken a 2023, kashi 27 sun bai wa jami’in hanci.
Idan aka kwatanta da abin da aka saba gani a baya, hakan na nufin yawan biyan rashawa a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 23 tun daga 2019, lokacin da aka samu kashi 29 da suka ba da hanci.
A wuraren da kuma aka tambayi cin-hanci amma mutane suka ƙi bayarwa, an ba da cin-hancin fiye da sau ɗaya cikin haɗuwa uku (kashi 34 cikin 100) a 2023.
Sai dai kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen da aka nemi su ba da rashawar a 2023 sun ƙi bayarwa sama da sau ɗaya.
Kazalika, binciken ya gano cewa raguwar ba da rashawar ta fi yawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kashi 76, duk da cewa sauran yankunan sun samu sama da kashi 60 cikin 100.