Wannan kyauta dai ta janyo cece-kuce da suka da dama daga ‘yan Najeriya musamman daga yankin Arewacin kasar.
Lamarin ya janyo muhawara mai ƙarfi a tsakanin mutane masu bambancin ra’ayi a kan wannan ƙayatacciyar kyauta.
An ƙiyasta cewa kuɗin motar ya kai kimanin Naira Miliyan 80 a yanzu haka a kasuwa.
Wannan kuɗi ya sa da dama na ganin kyautar ta wuce ƙima musamman duba da kuɗin da kuma shekarun yarinyar.
Ahmad Abdulhamid a ƙarƙashin labarin da Aminiya ta wallafa a shafinta cewa ya yi, “Wannan gaskiya ne Allah ya biya ’yar Baba ki ji daɗin mota lafiya komai lokaci ne yau kai ne gobe ba kai ba ne.”
Dawood Oumar kuwa tambaya ya yi da cewa, “To idan ta kammala jami’a jirgi zai ba ta ko?”
Muhsin Ibrahim shi kuma a nasa shafin na Facebook haka ya ce “Ba laifi ba ne yi wa ’yarka kyauta. Wataƙila ma da kuɗinka na kasuwanci ko wata harkar ka sayi motar. Amma mene ne na nuna wa duniya, a irin wannan yanayi da ake ciki a ƙasa?
Ibraheem Mu’azzam a nasa ra’ayin cewa ya yi: “Magana ta gaskiya, Yusuf Gagdi ya yi kuskure matuƙa wajen saya wa wannan yarinya mota tare da nuna ta a kafar sada zumunta domin al’umma su gani.”