Yan sama jannatin da suka maƙale a sama ba za su sauko ba sai a shekara mai zuwa

Spread the love

Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, NASA ta ce ‘yan sama jannatin nan biyu da suka maƙale a tashar sararin samaniya ba za sauko ƙasa ba, sai a cikin watan Fabrairun shekara mai kamawa.

Shugaban hukumar, Bill Nelson ya ce kumbon ‘Boeing Starliner’, da ya kai ‘yan sama jannatin cikin watan Yuni zai sauko ƙasa ba tare da kowa a cikinsa ba.

Ya ƙara da cewa a yanzu wani kumbon ne mai suna ‘SpaceX craft’ zai sauko da mutanen biyu,

Tun da farko dai an tsara mutunen biyu Barry Wilmore da Sunita Williams, za su yi kwana takwas a tashar samaniyar, kafin su fuskanci cikas bayan bulaguron nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *