Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wata matar aure mai suna Hafsat Surajo mai shekaru 24, bisa zargin ta da aikata laifin kisan kai.
Ana zargin Hafsat da hallaka Nafi’u Hafiz ta hanyar daddaba masa wuka a sassan jikin sa,wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa a yankin Unguwar uku karamar hukumar Tarauni.
Tun bayan faruwar lamarin ne jami’an yan sanda suka garzaya da shi,Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Hafsat Surajo ta bayyana wa Idongari.ng, cewa, a lokuta da da dama tana yin yunkurin hallaka kanta amma Nafi’un ne yake hana ta.
Ta kara da cewa, kafin abun ya faruwa ta dauko wuka domin kashe kanta , amma yaron gidan nata ya hanata harma ya karbe wukar daga hannun ta.
Sai dai daga baya a lokacin da yake yin bacci ne ta caccaka masa wuka a sassan jikinsa kuma lokacin mijinta baya gidan sai dai ta fada masa abunda ya faru.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya shaida Idongari.ng, cewa wadda ake zargin ta amsa laifin ta, inda ta tabbatar da cewa ta yi hakanne saboda shi yake hana ta kasha kanta.
Sai dai wata majiya da ba a tabbatar da labarin ba ,na cewa hatta iyayen ta sun san tana fama da damuwa, ya yin da wasu kuma ke cewa har wajen magani an taba kaita sakamakon zargin cewar tana fama da Aljanu.
Kwamishinan yan sandan ya ce bayan binciken da suka gudanar, sun gano mijin matar mai suna Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma wani Mallam Adam, nada hannu a yunkurin binne marigayin ba tare da sanin yan uwansa ba.
Mijin matar ya bayyana cewa, ya fara kiran yan uwan marigayin a waya da suke can jahar Bauchi inda ya fada musu cewar ya rasu amma bai sanar da dasu musabbabin rasuwarsa ba.
Ya kara da cewa marigayin shi ne yake kular masa da wasu kayayyakin kasuwancin sa, sai dai mijin matar da ake zargi ya ce, matar tasa tasha furta masa kalaman kisan ko kuma ta yi yunkurin kashe kanta.
Mallam Adamu da ake zargi da yi wa Nafi’u wankan Gawa , ya shaida wa Idongari.ng cewa mijin matar ne, ya kira shi a waya har ya bayyana masa cewar, an yiwa marigayin aikin Basir amma ya mutu.
Ya kara da cewa bayan yaje gidan ne sai yaga jikinsa da alamun yankan wuka, bayan ya tambayi mijin matar , sai ya shaida masa cewa matarsa ce ta caccaka masa wuka.
Mallam Adamu ya ce, ganin abunda ya faru ne ya ce mu su ,ba zai iya ba,amma sai matar ta ce matukar ba iyi wankan ba zata kashe kanta, shi kuma ganin ta furta kalaman kisa ne yasa shi yin wankan.
Tuni dai dukkan wadanda ake zargi suka bayyana nadamar su, inda rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.
IDONGARI.NG