Yan sandan jihar Yobe sun kama Lakcara kan zargin kashe matarsa

Spread the love

Rundunar yan-sandan Nigeria reshen jihar Yobe ta kama wani malamin Jami’a mai suna Abubakar Musa sakamakon kisan gilla da aka yi wa mai dakinsa.

Abubakar Musa da matar ta sa mai suna Ammi Mamman dukkanninsu malamai ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke Jami’ar jihar Yobe.

Mai magana da yawun rundunar DSP Dungus Abdukkarim shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar juma’a a birnin Damaturu.

A cewarsa, wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 4 da mintuna 48 na daren Alhamis a gidansu da ke rukunin gidaje na Bra-Bra da ke Damaturu.

DSP Dungus Abdulkarim ya ce, tun farko an kira yan-sanda an sanar da su cewa, an kashe wata mata a wani gida da ke unguwar ta Bra-Bra.

Ya ce, bayan isar ‘yan-sanda wajen da lamarin ya faru ne sai su ka samu marigayiya Ammi Mamman kwance shame-shame cikin jini, da alamar an caka mata wani abu mai kaifi a wuyarta, wanda wannan ne ya yi sanadiyar mutuwarta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan-sandan na jihar Yobe ya ce, an kama mijin marigayiyar ne saboda yana tare da ita suna kwance akan gado lokacin da lamarin ya faru.

Sai dai ya ce, tuni sashen bincike na rundunra ya yi nisa wajen bincike domin yadda kisan ya faru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *