Yan sanda a Kaduna sun kuɓutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi a Abuja

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kuɓutar da wani mutum da masu garkuwa da mutane suka kama a Abuja suka kuma nufi jihar da shi.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kuɓutar da mutumin wanda aka yi garkuwa da shi a Abuja babban birnin ƙasar ranar Laraba da maraice.

Rundunar ta ce a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ta samu rahoton yin garkuwa da wani mutum a Abuja, inda aka yi zargin masu garkuwar sun tafi da mutumin da suka sacen zuwa jihar Kaduna.

Daga nan ne rundunar ta ce jami’anta suka riƙa sanya idanu kan zirga-zirgar motocin da ke shiga jihar daga birnin na Abuja.

Sanarwar ta kuma ce da misalin ƙarfe 1:00 na rana ne jami’nta suka tare wata mota ƙirar Toyota mai launin ruwan toka, wadda ke ɗauke da mutum huɗu ciki har da direban, inda suka yi zargin masu garkuwar ne a ciki.

Yayin da mutanen suka ga ‘yan sanda sun tare su sai suka yi yunƙurin tserewa, inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe wuta wa ‘yan sandan, waɗanda su ma nan take suka mayar da martani.

Inda ɓangorin biyu suka buɗe wa juna wuta, lamarin da ya sa ‘yan sandan suka ƙubutar da wanda aka yi garkuwar da shi mai suna Segun Akinyemi da ke zaune a unguwar Area 3, Garki Abuja, tare da kama ɗaya daga cikin masu garkuwar mai suna Chinaza Philip da ke unguwar Life Camp a Abuja, inda sauran mutum uku suka tsere, waɗanda rundunar ta ce tana ci gaba da farautarsu.

Rundunar ta kuma ce ta ƙwato motar wadda ta mutumin da aka yi garkuwar da shi ne, da kuma ƙananan bindigogi nau’ikan Pistol da harsasai masu yawa daga wajen masu garkuwar.

Binciken farko ya nuna cewa maharan sun kama mutumin ne ranar Laraba 17 ga watan Janairu lokacin da ya fita daga gidansa da yamma.

Maharan na kan hanyarsu ta kai mutumin zuwa Kano a lokacin da ‘yan sandan suka kama shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *