Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

Spread the love

Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 da aka yi garkuwa da su a sansanin masu garkuwa da mutane da ke tsaunin Gongomaliki a yankin ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar Taraba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, David Iloyanomon, ne ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a birnin Jalingo.

A rufe duka layukan da ba haɗa da NIN ba – NCC

Kwamishinan ya ce jami’an sun samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukna ɓata-garin a yankin.

“Wannan na daga cikin yunƙurin da hukumarmu ke yi na kakkaɓe ayuukan ɓata-gari, musamman garkuwa da mutane da fashi da makami da satar shanu da ke addabar jiharmu,” in ji CP David Iloyonomon.

Ya ƙara da cewa hukumar ‘yan sanda ta ɗauki matakan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kamar mafarauta da ‘yan sa kai domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Jihar Taraba na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, da ‘yan fashin daji da masu satar shanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *