Yan Sanda  Fara Kama Wadanda Suke Da Hannu A Fadace-fadacen Unguwanni A Kano.

Spread the love
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin Yan sandan Kano

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta fara kama wadanda ake Zargi da hannunsu , a fadace-fadace dake Tsakanin wasu batagarin matasan unguwannin, Kofar Mata, Yakasai da kuma bangaren Zage da Zango da kewayensu , a cikin birnin Kano.

Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan, a wata tattauna da ya Yi da Jaridar idongari.ng, a ranar Laraba.

Kiyawa ya ce binciken ya gano cewa batagarin, na yin amfani da damar don satar kayan mutane.

Rundunar ta kara da cewa bayan girke jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya, an ci gaba da ganawa da al’ummar unguwannin, Inda kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin fara kama wadanda suke da Hannu, a cikin wannn tashin hankali kuma a Gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Haka zalika Rundunar ta Nemi Goyon bayan al’ummar unguwannin don magance matsalolin Baki daya .

A karshe kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya godewa Gwamnatin jahar da kuma al’umma bisa Goyon baya da ake ba su a kowanne lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *