Yan sanda na neman dangin matashin da ya yi fashin waya mota ta karya masa baya garin gudu a Kano

Spread the love
Kakakin yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta yi kira ga yan uwan matashin nan da ya gamu da tsautsayin karyewar baya da samun mummunan rauni akan sa , sakamakon takashi da wata mota ta yi lokacin da yake kokarin guduwa da wayar wata mata da ya kwace a ranar lahadin da ta gabata da suje ofishin yan sanda na Kwalli don bibiya.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin faifan murya mai minti daya sa dakika goma sha daya, da ya aikewa da Idongari.ng, da yammacin ranar litinin.

TALLA

Kiyawa, ya ce a saboda haka suke kiran yan uwan matashin ko wani da ya san, an nemi dan uwansa sanye da farar Riga da bakin Wando, da su garzaya wajen jami’an yan sandan.

Lamarin ya faru ne , a ranar lahadi 14 ga watan Janairun 2024 da misalin karfe 7:30pm .

” Mun samu kira na gaggawa daga unguwar Zoo Road, cewar wani matashi mai shekaru 25 zuwa 30, sanye da farar Riga da kuma bakin wando, ya yi wa wata mata fashi da makami da Danbuda inda ya kwace wayarta”SP Abdullahi Kiyawa”.

Sai dai a kokarin da yake yi na tsallaka Titi dan ya gudu mota ta bige shi.

Ya kara da cewa bayan samun rahotanne kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura dakarun yan sanda zuwa wajen da gaggawa, inda aka dauke zuwa babban Asibitin Murtala Muhammed dake birnin Kano, inda likita ya tabbatar da cewar kashin bayansa ya karye tare da samun mummunan rauni akansa.

An jima dai ba a ji , duriyar masu kwacen waya ba a birnin Kano sakamakon matakan da rundunar yan sandan jahar ta dauka, bisa jagorancin kwamishinan ta CP Muhammed Usaini Gumel, na zama da masu ruwa da tsaki, matasa, sarakuna, Malamai, kungiyoyi da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *