Yan sanda sun bayar da umarnin kama motoci marasa lamba a Abuja

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Abuja, ta bayar da umarnin kama duka motoci marasa lamba da ke yawo a faɗin birnin.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce kwamishin ‘yan sandan birnin, CP Benneth C. Igweh ne ya bayar da umarnin don kakkaɓe ayyukan ɓata-gari da ke fakewa da tuƙin mota suna cutar da al’umma.

“Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta damu matuƙa kan yadda ake tuƙa wasu motoci a birnin da lamba ɗaya kacal a jikinsu, da ma waɗanda ba su da lambar har fiye da lokacin da doka ta yarje, wato ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na maraice, kamar yadda sashe na 25 (5) na dokar sufurin birnin Abuja ta 2005 ta tanada”, in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun kuma aike da makamancin wannan gargaɗi ga masu sayar da motoci, sannan ta yi kira a gare su don kauce wa ajiye motocinsu a wurin da doka ba ta amince da hakan ba.

Sanarwar ta ce an ɓullo da dokar ce domin kakkaɓe ayyukan ɓata-garin da ke fakewa da hakan wajen cutar da al’umma.

“Ba sabon abu ba ne yadda ake samun matsalar fashi a cikin motocin da aka fi sani da ‘one chance,’ inda galibi ke amfani da motoci marasa lamba ko masu lamba guda wajen aikata laifin. Wannan aika-aika na ci gaba da sanya fargaba a zukatan al’umma, waɗanda ke ci gaba da aza ayar tambaya kan abin da ya sa har yanzu ‘yan sanda suka kasa magance matsalar”, in ji ‘yan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *