Ana Zargin Ango Da Kunna Wa Gawar Matarsa Mai Juna 2 Wuta Bayan Ya Halaka Ta

Spread the love

Jami’an yan sanda sun kama wani mutum mai suna, Motunrayo Olaniyi, dan shekaru 34 a duniya, bisa zarginsa da Dabawa matarsa mai juna biyu wuka, sannan ya kunna wa gawarta wuta a yankin Ikorodu dake jahar Lagos.

Sabbin ma’auratan sun yi aure ne watanni uku da suka gaba ta, inda mijin yake zargin ta da neman maza har ta samu juna biyun a yawon banza.

Lamarin ya faru a ranar juma’ar da ta gabata da misalin karfe 1:00pm na rana, bayan wata sa’insa ta kauce a tsakaninsu, inda ya zarge ta cewa cikin da take dauke dashi ba na sa ba ne, amma na dan uwansa ne, inda ita kuma Olajumoke ta musanta zargin da yake yi mata.

Wata majiya ta tabbatar da cewa sabon angon ya fara kaiwa amaryar tasa farmaki, a lokacin da mahaifiyar ta, ta ziyarcoi gidansu sakamakon sa’insar da ta kaure a tsakaninsu.

Makocin ma’auratan da ya bukaci a sakaya sunansa , ya bayyana cewa, sun yi auren gargajiya watanni uku da suka gabata, kuma Olajumoke tana dauke da cikin wata uku, inda daganan matsalar rashin fahimtar junan ta samo asali.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Legos, SP Benjamin, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce sun kama wanda ake zargin.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *