Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum 11 da zargin safarar miyagun ƙwayoyi a wasu samame da ta kai a wasu lokunan birnin.
Wata sanarwa a shafukan sada zumunta ta ce samamen sun kai ga gano buhun tabar wiwi 68.
“Kamen wani ɓangare ne na yunƙurin daƙile ayyukan safara na gungun ‘yanƙwaya da kuma rage aikata laifukan da shan ƙwaya ke haifarwa a birnin,” in ji SP Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar a Abuja.