Yan sanda sun cafke gungun mutanen da ake zargi da kasuwancin sassan jikin Bil’adama a Ogun

Spread the love

Yan sanda a jihar Ogun sun ce sun kama wani gungun mutane da suka ƙware wajen cinikin sassan jikin bil adama domin yin tsafi.

Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Abiodun Olamutu ya ce daga cikin abubuwan da aka gano a hannun mutane har da zuciyar bil adama da jarkoki biyu cike da sassan jikin bil adama.

Alamutu ya ce rundunar ta samu rahoton ɓatan wata mata masi suna Ms Sulaiimon Adijat ranar 9 ga watan Janairu bayan wani Adebayo Azeez ya gayyace ta.

Gwamnati ta rufe katafaren shagon Sahad stores a Abuja

Hukumar Hisbah a Kano ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta a fanfen bidiyo cewar duk namijin da zai aure ta sai ya kawo macen da za su yi latata.

A bayanin kwamishinan, an yi ta kiran wayar matar tun lokacin da aka ba da rahoton ta ɓata amma ba a same ta ba kuma a cewarsa, hakan ne ya sa jami’an da ke yaƙi da masu sace mutane suka baza komarsu domin gano abin da ya faru da ita.

Ya ƙara da cewa, binciken da aka yi ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna cikin wata ƙungiyar asiri mai suna ‘Oshole’ domin su haɗa naira miliyan ɗari biyu cikin mako ɗaya.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce duka mutanen da ake zargi sun amsa aikata laifin da ake zarginsu da shi. Ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi da suka tsere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *