Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Bisa Zargin Shirya Taron Gangi Da Ya Janyo Rikicin Fadan Daba A Kano.

Spread the love
CPM.U GUMEL

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta tabbatar da cafke wani mai suna, Muhammad Barde, mazaunin Unguwaar Darmanawa a karamar hukumar Tarauni, bisa zarginsa da hada taron Gangi, a bikin Yayansa, wanda ya haifar da ricikin fadan Daba, da ya yi sanadiyar rasa rayukan matasa biyu da asarar dukiya.

Kakakain rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai da safiyar Litinin.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Mayu 2024, a wajen taron Gangin da Magidancin ya hada, inda Yan Daba suka fito da makamai suka farwa al’umma har aka jikkata mutane uku, sannan kuma wasu mutane 2 suka rasa rayukansu da kuma Farfasa Motocin jama’ar yankin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya kara da cewa, kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayar da umarnin kama wanda ake zargi da shirya taron Gangin tare da karin wasu mutane 2 wadanda yanzu haka suke tsare a wajen yan sanda don gudanar da bincike.

Wadanda suka rasa rayukansu, sun hada da Sadiq Abdulkadir Darmanawa, mai shekaru 23 da kuma Muhammad Sani Sallari mai shekaru 22.

Tawagar hukumomin tsaron sun kwace makamai da dama an hannun Batagarin, tare da kwantar da hankulan al’ummar yankin.

A karshe rundunar yan sandan ta ce batun yana sashin gudanar da bincike, kuma da zarar an kammala za a sanar da jama’a halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *