Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Yin Garkuwa Da Yaro Sannan Ya Nemi Kudin Fansar Miliyan 50 A Kano.

Spread the love

Rundunar yan Sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama Wani matashi Mai suna Abubakar Musa, Dan Shekaru 25 mazaunin unguwar Rijiyar Lemo Kano, bisa zarginsa da yin Garkuwa da Karamin Yaro Mai shekaru biyu da rabi, har ya nemi kudin fansar Naira Miliyan hamsin , Kafin ya saki yaron Mai suna Al’amin Ahmed Garba.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce sun kama Wanda Ake Zargin a ranar 25 ga watan Disamba Shekarar 2024, a unguwar Liman Dorayi, bayan samu bayanan sirri na gidan da yake boye da Yaron tsawon kwanaki Uku.

Sanarwar ta kara da cewa,  jami’an Yan Sanda Sun kubutar da Yaron sannan suka Kai shi, asibitin Kwararru na Murtala Muhammed Kano, Inda aka duba lafiyarsa sannan aka mika shi Hannun iyayensa.

Tun a ranar 3 ga watan Janairun 2025, Rundunar suka Gurfanar da matashin a gaban kotun majistire Mai 25 dake unguwar NormanSland don ya fuskanci hukunci.

Kwamishinan Yan Sandan Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ce za su ci gaba da jajircewa don tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *