Yan sanda sun cafke matashin da ya nemi kudinsa fansa 1m bayan ya yi garkuwa da kaninsa a Kano.

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Kano ta tabbatar da kama wani matashi Salisu Adamu mai shekaru 18, mazaunin karamar hukumar Danbatta Kano bisa zargin sa da hannu dumu-dumu na yin garkuwa da Dan gidan kanwar mahaifiyarsa mai shekaru uku a duniya.

Mahaifin karamin yaron Mallam Aminu Garba Danbatta , shi ne ya shigar da korafin sa ga jami’an yan sanda tun a ranar 19 ga watan Disamba 2023 kan batan dan nasa Auwalu Aminu mai shekaru 3.

idongari.ng, ya ruwaito cewar wanda ake zargi ya kira waya da boyayyiyar namba , inda ya bukaci a baya shi kudin fansa ,naira miliyan daya 1, 000, 000:00, kwanaki biyar da sace shi.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa tunda suka samu rahotan yin garkuwa da yaron suka shiga farautar wadanda ake zargi da aikata laifin, kuma Allah ya ba su basarar cafke matashin tare da kubutar da karamin yaron a karamar hukumar Gwale Kano cikin koshin lafiya.

Wanda ake zargin ya tabbatar wa da idongari.ng, cewar shi ne ya yi garkuwa da yaron ba tare da sa hannun kowa ba.

ya kara da cewa , zai yi amfani da kudin ne wajen biyan bashin da ake binsa sama da naira dubu dari sakamakon karyewar kasuwancinsa.

Sai dai bai kai ga karbar kudin ba jami’an yan sandan suka yi nasarar cafke shi.

Mahaifin karamin yaron Mallam Aminu Garba, ya bayyana takaicin sa, da crwar wanda ake zargin dashi ake neman bacewar dan na sa , sai dai ya godewa jami’an yan sandan jahar Kano bisa kokarin da suka yi wajen ceto dan nasa a hannun mai garkuwa da mutanen cikin aminci.

A karshe kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ya ce da zarar sun kamma bincike za su gurfanar da shi a gaban kotu dan ya fuskanci hukunci.

idongari.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *