Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane 15 da ake zargi da aikata laifuka maban-banta da suka hadar da yan fashi da makami, barayin ababen hawa, masu barnata wayoyin ba wa fitulun haska tituna, da kuma barayin wayoyin salula da daidai sauran su.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Jigawa ASP Abubakar Isah , ya sanya wa hannu tare da raba wa manema a ranar Asabar.
Sanarwar ta kara da cewa daman ta dade tana neman Yusuf Yusuf mai shekaru 25 mazaunin Garin Katoge a karamar hukumar Kazaure ta jahar Jigawa da kuma Umar Abubakar mai shekaru 23 mazaunin kauyen Dakayya a karamar hukumar Kaugama dake jahar da ake zargi da aikata laifin fashi da makami.
Idan ba a manta ba, a ranar 19 ga watan Julin 2023, rundunar ta samu kiran gaggawa da cewar wasu mutane dauke da makamai su 5, sun shiga gidan wani mai suna Sunusi Hudu, inda suka yi masa duka tare da yi masa fashin Mota kirar Honda Accord 2011, Plasma Tv guda 2 , Laptop 1 da kuma wayar hannu kirar Redmi Note 11pro.
Bisa bayanan sirri da rundunar yan sandan jahar ta samu ta cafke mutane 4 daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin.
Haka zalika jami’an yan sandan sun cafke wani mai suna Yakubu Hamza , da ake zargi da yin amfani da Diga yana hake wayoyin cable da suke bayar da hasken wutar kan Tituna.
Duka wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zargin su da aikata wa , kuma rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci .