Jami’an yan sandan jahar Kano, sun kama wasu matasa hudu da ake zargi da aikata laifukan fashi da makami da kuma satar shanu.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da jaridar www.idongari.ng, a ranar Alhamis.
Tun a ranar 6 ga watan Nuwamban 2024, da misalin karfe 5:30pm , jami’an yan sandan suka samu sashihan bayanai kan wadanda ake zargin inda aka kama daya daga cikinsu mai suna Bayero Shu’aibu,wanda akafi sani da Bera, mazaunin Garin Fanteka dake karamar hukumar Gabasawa Kano.
Haka zalika an cafke, Sa’idu Muhammad, da ake kira Gati, Aliyu Umar da kuma wani mutum daya, dukkansu mazauna garin Majawa a karamar hukumar Warawa ta jahar.
- Cikin Hotuna : Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Mutane 82 Da Zargin Aikata Laifuka Mabambanta.
- Marayu Sama Da 50 Ne Suke Korafin Matashin Da Ake Zargi Da Karbe Wayoyinsu Don Ba Su Tallafi.
Sanarwar ta ce wadanda ake zargin sun kware wajen aikata laifin fashi da makami, a yankunan kananan hukumomin Gabasawa da kuma Wudil.
Binciken yan sandan ya gano bindiga kirar AK-47 1 da kirar gida guda 1 sai kuma bindigar Harbin tsintsaye 2.
A karshe rundunar ta ce wadanda ake zargin sun amsa laifin kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.