Yan Sanda Sun Cafke Mutane 54 Da Ake Zargi Da Yunkurin Hana Gudanar Da Hawan Daushe A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu yan Dabar siyasar 54, dauke da muggan makamai da kwayoyi a ranar Idin Sallah tare kuma da gano yukurin da wasu ke yi na  hana gudanar da bikin hawan Daushe  a fadar sarkin Kano a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2024.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa jaridar idongari.ng, a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce rundunar yan sandan ta gano makircin da wasu marasa kishin Kano da zaman lafiyarta ke shiryawa ne ya basu damar kara yawan jami’an tsaro don kare rayukan al’umma da dukiyoyin tare tabbatar da an kammala bukukuwan sallar lafiya.

SP Kiyawa, ya ce daman hukumomin tsaron jahar suna sane da yadda batagarin ke shirin tayar da hankulan al’umma  wajen fakewa da rigar siyasa a yayin hawan Hawan Daushen, inda ya ce akwai isassun jami’an tsaro da na’urorin da za su dinga ba su bayanan yadda abubuwa suke kasancewa a wurare daban-daban.

Rundunar yan sandan ta lashi takobin kama duk wanda ya yi yunkuri kawo rashin zaman lafiya da jahar , don ya fuskanci hukunci tare da ma su daukar nauyin su.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce bukin sallah lokaci ne na farin ciini  da ziyarar yan uwa, kuma wajen bikin hawan Daushe waje ne na nuna al’adu ba  harkokin siyasa ba, da wasu magoya ke nuna fastocin siyasa da alluna, inda ya shawarce su da su kiyaye aikata hakan don ba daidai ba ne.

Mutane 54 da rundunar ta cafke a ranar sallar Idi , suna ci gaba da amsa tambayoyi kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

A karshe rundunar ta bukaci al’umma da su kwantar da hankulansu , su ci gaba da gudanar da shagulgulan sallar ba tare da wani jin tsoro ba, ta kuma shawarci jama’a da zarar sun ga wani abu da basu amince da shi ba, su gaggawar sanar da ita ta wadannan hanyoyi.

08032419754, 08123821575, 09029292926, or log-in to the NPF Rescue Me Application available in the Play Store, or through the following Online Media Platforms:

Facebook: Kano State Police Command

Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)

Instagram: Kano State Police Command

Tiktok: Kano State Police Command.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *