Rundunar yan sandan jahar Nasarawa ta kama wani sojan bogi mai suna Muhammed Halidu dake jahar .
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a lafiya babban birnin jahar, inda ya ce sojoji ne suka kama wanda ake zargin sanye da kakin sojoji a karamar hukumar Awe kuma suka mika wa jami’an yan sanda shi domin gudanar da bincike.
Ya kara da cewa , ya na bayyana kansa a matsayin jami’in soja daga runduna ta 231 a Biu dake jahar Borno.
Sai dai binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa sojan yake yi tare da cutar da al’umma.
” binciken mu ya nuna mana cewa ya cuci al’umma ta hanyar damfarar su”.
Rahotanni na cewa wanda ake zargin ya yi kokarin shiga aikin sojan , amma bai samu nasara ba inda ya koma yake yin sojan gona amatsayin jami’in soja.