Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka mabanbanta a fadin jahar.
Bayanin hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a rundunar yan sandan jahar Jigawa ASP ABUBAKAR ISAH, ya raba wa manema labarai a ranar Talata.
Cikin wadanda rundunar ta cafke sun hada da yan fashi da makami, barayin ababen hawa, barayin wayar salula da masu barnata waya ceble.
Sanarwar ta kara da cewa, an samu nasarar kwato bindigu kirar gida guda 2, barura masu kafa biyu 11 da dai sauransu.
Wannan na zuwa ne a lokacin da rundunar yan sandan ke ci gaba da yaki masu aikata laifuka a fadin jahar, inda ta samu nasarar kama wadanda ake zargin a sassan Dutse, Kazaure, Maigatari, Gwiwa, Malam Madori , Kiyawa, Birniwa da kuma Garki.
Cikin wadanda rundunar ta cafke sun hada gungun wasu matasa da suka shiga gidan wani magidanci dauke da muggan makamai har suka yi masa fashin kudi naira miliyan daya da dubu dari biyar , sannan kuma suka tursasa shi ya kai su gidan mahaifiyar sa , suka karbi kudi sama da naira dubu dari biyar da tafiya da Baburan hawa guda 2.
A karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.