Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kitsa Fadan Daba Tsakanin Matasan Zango Da Kofar Mata.

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa biyu, wadanda ake zargi da jagorantar fadan daba tsakanin unguwannin Kofar Mata da Zango a karamar hukumar birnin Kano.

Dakarun yan sandan da aka girke a mahadar Kofar Mata kusa da unguwar zango da kuma asibitin kwararru na Murtala Muhammed ne, suka kama matasan a ranar 24 ga watan Disamba 2024, da misalin karfe 8:40pm na dare.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya tabbatar da kama matasan wadanda suka hada da, Kabiru Jamilu, da akafi sani da ( AWU) mai shekaru shekaru 21 da kuma Umar Garba dan shekaru 32, dukkansu mazauna unguwar Zango kamar yadda jaridar idongari.ng ta ruwaito.

Binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa, Kabiru, ne ya kitsa rikicin Dabar da ya barke tsakanin matasan Kofar mata da kuma Zango, haka kuma shi ne ya jagoranci fadan daba a lokacin da ake gudanar da bincike.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an dawo da matasan babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka na CID, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

A karshe kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya bukaci mazauna kofar mata da Zango , su kasance masu ba wa yan sanda hadin kai, musamman  wajen bayar da bayanan sirri don magance matsalar baki daya.

Ga Nambobin kiran gaggawa, 08032419754, 08123821575, 09029292926.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *