Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta samu nasarar Kama wasu mutane, da ake zargi da damfarar yan kasuwa ta hanyar tura mu su , Alert na bogi bayan sunyi siyayya a wajensu.
Kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai, a da yammacin Ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce , a ranar 5 ga watan Yuni 2024, ne rundunar ta samu kiran gaggawa daga manajan gidan man Chula, cewar wadanda ake zargin sun sayi man Diesel, na dubu dari uku (300,000:00) inda suka biya kudin ta hanyar tura Alert na bogi.
- Ba za mu iya biyan mafi ƙanƙantar albashi na N60,000 ba – Gwamnonin Najeriya
- An ɗage sauraron ƙarar da Sarki Aminu Ado Bayero ya shigar
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya Kara da cewa bayan samun rahotan ne, Kwamishinan Yan Sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, ya tashi dakarun yan sanda don kamo wadanda ake zargin a duk inda suke.
Binciken yan sanda na farko-farko ya kai ga Kamo mutane biyu, da suka hada da , Abdulkadir Ibrahim mai shekaru 38, Mazaunin Unguwar Na’ibawa da kuma Aliyu Tukur dan shekaru 27 dake zaune a Kuntau Kano.
Haka zalika matasan da aka cafke sun jagoranci yan sanda, inda aka Kamo wani Auwal Ibrahim Mazaunin Na’ibawa, Wanda aka samu man Diesel din a wajen sa.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu, sun hada da POS 22, Katinan cirar kudi (ATM ) 52 , wayoyin salula 6 da kuma Harkokin man Diesel guda 8.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, wadanda ake zargin sun amsa laifin su, tare da tabbatar da cewa, sun damfari ma’aikatan gidajen da dama da suka hada da A.Y. Maikifi, Aliko da kuma sauran yan kasuwa dake jahar.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaki da Masu aikata laifuka a fadin jahar.
Yanzu haka matasan da ake zargin suna sashin binciken manyan laifuka na CID, don fadada bincike akan su kuka da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.
A karshe Rundunar ta an karar da yan kasuwa da sauran su rinka kula da batagarin mutane wadanda za su zambace su ya yin gudanar da kasuwancinsu.
Kwamishinan Yan Sandan ya godewa al’ummar Jahar Kano, bisa hadin Kai da goyon bayan da suke ba wa Rundunar a koda yaushe.
Rundunar ta bayar da nambobin karta kwana domin don sanar da ita wani Abu da ba a amince da shi, 08032419754,08123821575 ,09029292926.