Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Da Halaka Kakanninsa A Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar rasuwar wasu aurata sakamakon zargin da ake yi wa jikansu da halaka su da wuka.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata snaarwa da ya rabawa manema labarai yau Alhamis.

Sanarwar ta ce sun samu labarin mara dadi daga Kofara Dawanau dake karamar hukumar Dala Kano, inda ake zargin matashin mai suna , Mutawakilu Ibrahim dan shekaru 30, da yin amfani da wuka ya caccakawa kakanninsa a sassan jikinsu saboda wani sabani wanda hakan ya yi sanadiyar samar musu da munanan raunuka.

SP Abdullahi Kiyawa , ya kara da cewa an yi gaggawar garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu , kuma an mika gawar mamatan da iyalinsu don yi musu jana’iza daidai da koyarwar addinin musulinci.

Binciken farko-farko da jami’an yan sanda suka gudanar ya tabbatar da cewa ya aikata laifin ne sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi, kuma tuni kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya bayar da umarnin dawo dashi sashin gudanar da binciken laifukan kisan kai don fadada bincike kafin a gurfanar dashi a gaban kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *