Yan sanda sun cafke wani lauya bisa zarginsa da yi wa matarsa dukan kawo wuka.

Spread the love

Wani lauya mai ya shiga hannun ’yan sanda kan zargin lakada wa matarsa dukan kawo wuka a Jihar Akwa Ibom Nigeria

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Barista Sunday Ebong yana dukan matarsa, daga ita sai ’yar riga da dan kamfai a jikinta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, SP Odiko MacDon, ya ce “an kama Barista Ekeere Sunday Ebong ne bisa zargin lakada wa matarsa duka aka baza a kofofin sada zumunta, inda aka ga ya ji mata rauni lokacin da yake dukan ta, ya farfasa mata jiki.”

Kazalika ana zargin Barista Sunday da kasancewa mutum mai yawan cin zarafin matarsa.

Hukumar Hisbah a Kano za ta mayar da hankalin ta kan horas da Dakarun ta illimin aikin Hisbah a zahiran ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *