Yan Sanda Sun Cafke Wasu Matasa Da Ake Zargi Da Neman Juna A Gombe.

Spread the love

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama matasa biyu da ake zargi da neman maza.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a shelkwatar rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Yulin 2024, rundunar ta samu labarin  cewa an kama wadanda ake zargin suna neman juna a unguwar Kanbariki da ke garin Kumo.

Daga nan rundunar ta je wuri ta cafke wadanda ake zargin inda aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

Buhari ya bayyana cewa a lokacin da ake gudanar da bincike wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Ya ce daya daga cikinsu ya bayyana cewa dayan ya yi alkawarin ba shi kudi N15,000 idan suka kammala.

Amma bayan ya samu biyan bukatar tasa sai ya nuna masa cewa ba zai ba shi kudin ba.

Jami’in ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *