Yan sanda sun cafke Yan Daba 7 da ake zargi da yunkurin tarwatsa zabe a Yobe ta Gabas.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Yobe, ta cafke wasu mutane 7 da ake kyautata yan daba ne, a karamar hukumar Bade dake jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar, Dungus Abdulkarim , ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar, bayan jami’anta da na sojoji sun cafke su a wani aikin sintiri da suke gudanarwar.

Dungus Abdulkarim , ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a cikin mota kirar Bus mai daukar fasinjoji 18, a lokacin da suke yunkurin zuwa Damaturu domin tarwatsa zaben cike gibi a Yobe ta Gabas.

Abubuwan da suka faru a zaben cike gibin karamar hukumar Kunchi Kano.

Ya bayyana sunayen mutane 7 da suka hada da Abubakar Bololo mai shekaru 25, Habu Mato mai shekaru 35, Suleman Musa mai shekaru 50, Yusuf Danjuma mai shekaru  33, Abdullahi Haruna  mai shekaru 45,  Zainab Mohammed mai shekaru 25, da kuma Rachael Bitrus mai shekaru 23.

‘’ An kama su a ranar 3 ga watan Fabarairun 2024, da misalin karfe 7:00am na safe ‘’

A karshe ya ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *