Yan sanda sun ceto mutum biyu da aka sace a Abuja

Spread the love

Yan sanda sun yi nasarar ceto wasu mutum biyu da masu satar mutane domin karbar kudin fansa suka yi garkuwa da su a cikin daren da ya gabata na Talata 31 ga watan Janairu, 2024 wajen karfe 1:00 na dare, a Abuja.

Rundunar ‘yan sandan birnin na tarayya ta ce, ta shiga farautar barayin ne bayan rahoton da ta samu na satar mutanen biyu, Sarah Hassan da Madam Erima Bobo-John a kauyen Kobi da ke yankin babban birnin tarayyar.

Rundunar ta ce jami’anta da ke ofishin yanki na Asokoro ne suka shiga farautar barayin inda suka yi nasarar rutsa su a kan hanyar Nyanya zuwa Keffi inda sojoji suka tare barayin a wajen binciken ababen hawa.

Yan bindiga sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan gida daya a Abuja

Ba mu amince da wasu mombobin kwamitin albashi ba – Shugaban NLC

Sanarwar ta ce da ganin’yan sandan ne sai barayin suka bude wuta, inda ‘yan sandan suka rinjaye su, ganin haka barayin suka gudu ta dajin da ke kusa da wurin, suka bar mutanen da suka sata.

Tuni an mika mutanen biyu ga ‘yan uwansu ba tare da sun ji wani rauni ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *